• 18 Jun, 2025

Zan Toshe Ramuka 64 Da Ke Kan Titunan Najeriya—Cewar Ozohu-Salihu

Zan Toshe Ramuka 64 Da Ke Kan Titunan Najeriya—Cewar Ozohu-Salihu

1000004060.jpg

Matashiyar nan da ta lashe gasar sarauniyar kyau da masana'antar Nollywood ta shirya za ta fara aikin toshe ramuka da ke titunan Najeriya.

Miss Ozohu-Salihu za ta gudanar da ayyukan tushe ramukan ne a jihohin   Najeriya 36.

Matashiyar mai suna Ozohu-Salihu ta furta haka ne jiya Litini yayin da ta ke zantawa da yan jarida a birnin Lokoja da ke jihar Kogi, arewa maso tsakiyar Najeriya.

Ozohu-Salihu ta ce aikin na daya daga cikin ayyukan da zai faranta mata rai  domin aiki ne na ceton rayukan al-umma a kasar.

Miss Salihu ta ce, ta damu da afkuwar hadura a kan titunan kasar, haka ne ya sa ta yanke shawarar yin wannan aikin.

Ta ce, hakan zai taimaka matuka wajen rage asarar rayuka da ake samu a kowace rana a fadin Najeriya.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.