
Dan majalisar dattawa mai wakiltar Delta ta tsakiya Ede Definone ya bayyana dalilin da ya sa su ke neman gwamnati ta kirkiri jihar Anioma daga jihar Delta, inda ya ce, yin hakan adalci ne garesu.
Dafionone ya bayyana haka ne yayinda ya ke zantawa da manema labarai a garin Ugheli da ke jihar Delta jiya Litini, inda ya ce, kirkirar jihar zai kawo ci gaba matuka.
Sanatan ya kara da cewa, bada jihar Anioma zai habaka ci gaban yankin baki daya da 'yan kabilar Urhobo, wadanda su ne mafi yawa a yankin Naija Delta.
Dan majalisar ya ce, kabilar Urhobo wadda yawan al-ummarta ya kai sama da miliyan 10, za su samu bunkasar ci gaba a kananan hukumominsu guda 8 a jihar Delta da wasu yankunan jihar Bayelsa.
Neman jihar Anioma daga jihar Delta ya jawo cece-kuce musamman dangane da bukatar sake fasalta tsarin tarayyar Najeriya domin amfanin 'yan kasa.
Sanatan ya kara da cewa, a matsayinsa na dan Naija Delta ta tsakiya, ya na da yakinin fafutukar neman jihar Anioma zai kawo bunkasar yankin na Naija Delta ta hanyar cimma burinsu na kawo canji.