
Gwamnan jihar Sakkwato Ahmed Aliyu ya bada umarnin fara bawa shugabannin makarantun sakandaren jihar kudi alawus Naira 200, 000 kowani wata domin rage musu radadin matsin tattalin arziki.
Gwamnan ya furta haka ne yayin wata ganawa ta musamman da 'yan jihar Sakkwato kan kasafin kudin shekara mai zuwa da aka yi jiya Litini.
Gwamnatin jihar ta duba cancantar fara biyan kudaden ne bayan roko da tsohon mataimakin gwamnan jihar Chiso Abdullahi ya yi.
Da ya ke bayani a madadin gwamna Ahmed Aliyu, sakataren yada labarai Abubakar Bawa ya ce, gwamnan ya rantaba hannu akan biyan kudi Naira 200, 000 domin saukaka lamura.
Gwamnatin jihar za ta fara biyan Naira 200,000 ne ga kowani shugaban makarantan sakandare a fadin kananan hukumomi 23 na jihar, wanda za a fara a watan biyu na shekara mai zuwa.
Bawa ya ce kudaden za su taimaka sosai wajen kulawa da wasu daga cikin bukatun shugabannin makarantun.
Gwamnan ya kuma bawa kwamishinan kananan hukumomi Dadi Adare umarni ya yi nazarin kudaden sarakunan gargajiyar jihar domin duba yiwuwar kara musu, duba da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.
Rahotanni sun nuna cewa sarkin Kilgori Muhammad Jabbi, wanda ya wakilci Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ne ya nemi gwamnatin jihar ta duba karin kudaden nasu.