• 17 Jun, 2025

Karin Haraji Kan Lemon Kwalba Zai Iya Rage Cutar Sukari A Najeriya

Karin Haraji Kan Lemon Kwalba Zai Iya Rage Cutar Sukari A Najeriya

1000013263.jpg

Ana sa ran haraji da gwamnatin Najeriya ta kakaba kan lemon kwalba zai iya rage illar cutar sukari a kasar, duba da yadda ake kwankwadan lemon kwalbar a fadin Najeriya, daga kudu zuwa arewacin kasar.

Ciwon sukari na daya daga cikin matsalolin kiwon lafiya da jama'a ke fama da si, inda cutar ke habaka cikin sauri a duniya.

An tabbatar da cewa shan kayan zaki irin su lemon kwalba yana da alaka da tabarbarewar lafiya a cikin akasarin masu ciwon sukari da ma wadanda ke kamuwa da cutar.

Masana kiwon lafiya suna bayar da shawarar cewa rage shan wadannan kayan zaki, da cin ingantaccen abinci mai gina jiki, da kara yawan motsa jiki a matsayin dabarun inganta rigakafi da kuma dakile ciwon sukari.

Najeriya na da kaso mai tsoka na kasuwar lemon kwalba da kayan zaki ta duniya kuma ana hasashen wannan kaso zai iya kaiwa na Dalar Amurka biliyan 10 tsakanin shekarar 2021 zuwa 2026 a kasar.

Wannan wata alama ce da ke nuna cewa yawan shan sukari a cikin abubuwan sha na zama matsalar lafiyar jama'a da ke bukatar kulawar gaggawa da ke bukatar kudade masu yawa, wanda hakan ya sanya aka bullo da haraji na musamman kan lemon kwalba da sauran kayan zaki.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa, yawan mutanen da ke fama da ciwon sukari a duniya ya tashi daga mutane miliyan 200 a shekarar 1990 zuwa miliyan 800 a shekarar 2022, kuma yaduwar cutar ya fi muni ne a kasashe masu tasowa.

WHO ta kara da cewa kimanin mutane miliyan 24 ne ke fama da ciwon sukari a nahiyar Afirka, kuma ana hasashen wannan adadin zai karu da kashi 129 cikin 100 zuwa miliyan 55 nan da shekarar 2045.

Afirka ta kasance nahiya ta biyu mafi karancin kashe kudi kan batutuwan kiwon lafiya masu alaka da ciwon sukari, inda ake kashe Dalar Amurka biliyan 13, wanda ya kasance kashi daya kacal na kudasen da ake kashewa kan cututtuka masu alaka da ciwon sukari na duniya.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.