
Kungiyar rajin kare 'yancin danAdam wato Pyrates Confraternity a Turance, ta ja kunnen shugaba Bola Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan da karbo bashi banza-zanza.
Kungiyar ta bayyana haka ne a wata takarda da ta fitar wanda mai magana da yawunta Dakta Joseph Oteri ya sanyawa hannu a jiya Litini.
Kungiyar ta ce, karbo ranchen kudi har Dalar Amurka biliyan 2.209 domin cike gibin kasafin kudin bana babban kuskure ne da gwamnatin ke yunkurin yi.
Kungiyar ta furta hakan ne, daidai lokacinda bashin da ke kan gwamnatin Najeriya ya kai har Naira triliyan 134.
Kungiyar ta yi kaca-kaca da gwamnatin Tinubu kan dogaro da danyen man fetur, inda ta ce, fitarda man fetur kasashen waje ba shi ne mafita ba.
Kungiyar ta ce, akwai bukatar gwamnati ta lalubo hanyoyin samun kudaden shiga maimakon dogaro da man fetur a kasar.
Kungiyar ta nuna damuwanta dangane da hauhawan basuka da gwamnatin kasar ke ciyo wa ba tare da lissafi ba, wanda hakan barazana ce ga tattalin arzikin kasar.
Kungiyar ta ce, duk da cewa shugaba Bola Tinubu ya yi ikrarin bashin da ke kan Najeriya ya ragu daga kashi 97 zuwa 65 cikin 100, ci gaba da amsar bashi barazana ce ga kasar.
A nata bangaren, majalisar dokokin Najeriya ta bayyana cewa, yawan bashi da tazara da ke akwai wajen canjin kudin Najeriya ka iya jefa kasar a cikin masifa daga shekara mai zuwa zuwa shekarar 2027.
Majalisar dokokin ta zargi gwamnatin Tinubu da almabazzaranci da dukiyar kasar, inda ta ce, abin takaici ne duk da halin da Najeriya ke ciki, amma gwamnatin kasar na kara karban bashi domin cike gibin kasafin kudin 2024 da yin facaka.
Majalisar dokokin ta bawa gwamnatin tarayya shawarar dakatarda karban bashin, inda ta ce, ya zama dole gwamnatin ta rage almabazzaranci domin gujewa matsalar tattalin arzikin kasa da ba za a iya warware ta ba.