• 17 Jun, 2025

Gwamnatin Najeriya ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 220

 

Gwamnatin Najeriya ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 220 bayan sakamakon binciken da ƙasar ta gudanar wanda ya gano musayar bayanai da kamfanin ke yi ta kafofinsa na WhatsApp da Facebook sun saɓa wa dokar ƙasar.

Binciken wanda hukumar kare haƙƙin masu sayayya ta ƙasar ta gudanar ya zargi kamfanin Meta da yin amfani da ɗaukar bayanan mutane ciki har da na sirrinsu ba tare amincewarsu ba da kuma mamayar kasuwanci.

Hukumar ta kuma bukaci kamfanin ya biya ƙarin dala 35,000 na kuɗaɗen da ta kashe wajen gudanar da binciken.

Gwamnatin Najeriya ta ba kamfanin wa'adin wata biyu ya biya kuɗaɗen na tara. Babu wani martani da ya fito daga kamfanin kawo yanzu