
Babban Limamin addinin Kirista na Majami'ar Katolika da ke birnin Sakkwato, arewa maso gabashin Najeriya, Bishop Matthew Kukah, ya ce, babu wani shugaban kasa a Najeriya da ya shirya jagorancin kasar kamar shugaba Bola Tinubu.
Matthew Kukah ya furta haka ne yayinda ya ke gabatarda jawabinsa a wajen wani taro a karshen sati a Abuja.
Kukah ya bayyana cewa, duk wadanda su ka yi mulkin kasar a tarihin kasar ba su shirya ba lokacin da su ka hau karagar mulkin kasar.
Limamin Kiristocin ya ce, tun daga Ernest Shonekan har zuwa Olusegun Obasanjo, da Goodluck Jonathan da Umaru 'Yaradua da ma Muhammadu Buhari, babu daya daga cikinsu da ya shirya mulkin kasar.
Kukah ya ce, Shugaba Bola Tinubu ne kadai ya shirya kafin hawa mulkin kasar, amma abin takaici shi ma 'yan kasar na fama da wahalhalu tun hawansa karagar mulki.
Kukah ya nuna rashin jin dadinsa kan rashin ilimin shugabanci da rashin shiri da cancanta da ke shugabannin Najeriya ke fama da su, inda ya ce, banda burin azurta kansu da makusantansu, babu wani abu da shugabannin Najeriya su ka iya.
Bishop Matthew Kuka ya ce, ribar dimukuradiyya na da dama, ba kawai gine-gine ne ribar ba, inda ya ce, idan gine-gine ne ribar mulki, babu wanda yakai Adolf Hitler a tarihin duniya.
Matthew Kukah ya karkare da cewa, akwai abubuwa da dama da al-umma ke bukata domin rayuwarsu ta inganta, ba kawai gine-gine a kasa ba.