• 18 Jun, 2025

Za'a Tura Duk Wanda Ya Ki Karanta Sabon Taken Najeriya Gidan Kaso—Cewar Majalisar Wakilan Kasa

Za'a Tura Duk Wanda Ya Ki Karanta Sabon Taken Najeriya Gidan Kaso—Cewar Majalisar Wakilan Kasa

house-of-reps-2.jpg

Majalisar wakilan Najeriya za ta yi doka mai tsanani da za ta hukunta duk wanda ya ki karanta sabon taken kasar da gangan.

Dokar da ake shirin yin ta za ta tilasta wa mutum biyan kudi har Naira miliyan 5 ko zama a gidan maza na shekara 10 ko duka.

Dokar har wayau za ta tusa keyar duk wani dan kasa da ya lalata wata alama ta kasa mai daraja ko wuraren addinai zuwa gidan kaso ko biyan miliyan 5.

Kakakin majalisar Abbas Tajudeen ne ya gabatar da kudirin dokar wanda za'a mishi karantu karo na biyu kafin yan majalisan su yi mahawara akan shi.

Kudirin dokar zai hukunta ta hanyar tasa keyar duk wanda ya datse kan titi ko ya shirya wata tattaki gidan maza tare da biyar tarar kudi Naira miliyan 2.

Dokar za ta tura mutum gidan kaso bayan biyan tarar Naira miliyan 3 idan ya ci amanar kasa ta hanyar goyon bayan wata kungiya ko kasa sabanin kasar sa Najeriya.

Idan ba'a manta ba a watan 5 ne shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar dowo da tsohon taken kasar da aka bar amfani da shi tun shekarar 1978.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.