
Hukumar kula da harkar Sharia a Najeriya ta ce ta shirya gudanar da ganawa ranar Juma'a 16 ga watan Agusta domin yanke hukuncin wanda zai gaji babban alkalin alkalan kasar.
Alkalin alkalan zai yi ritaya ne ranar 22 ga wannan watan na Agusta yayin da ya cika shekaru 70 da haihuwa.
Wata majiya da ba'a bayyana ta ba daga ofishin babban alkalin alkalan ta tabbatar da zaman da za'a gudanar a ranar Juma'a don zaben magajin nashi.
Idan hukumar Shariar ta zabi magajin babban alkalin alkalan za ta aikawa shugaban kasa Bola Tinubu domin sanya hannu.