
Shugaban jami'ar jihar Yobe Farfesa Mala Mohammed Daura ya ce, sun shirya tsaf don taimakawa rundunar sojan Najeriya yaki da kungiyar Boko Haram a jihar Yobe da ma yankin arewa maso gabas baki daya.
Farfesa M. M. Daura ya furta haka ne yayin da Birgediya Janar EC Ineme ya kai mishi ziyara a jami'ar ta Yobe a birnin Damaturu.
Farfesa Daura ya ce, jami'ar su na da kwarewa da zarata da za su taimakawa sojojin ta fannin gudanar da bincike kan matsalar Boko Haram a jihar da ma sauran matsalolin yan bindiga a kasa baki daya.
M.M. Daura ya ce, kofar hukumar jami'ar a bude ta ke domin bada gudumawa kan batun rashin tsaro idan bukatar hakan ta taso don kawo karshen matsalar da ta shafe shekaru ta na addabar jihar da yankin da kasa baki daya.
A nasa bangaren EC Ineme ya ce, makasudin ziyarar sa zuwa ofishin shugaban jami'ar shi ne neman hada gwiwa domin kulla alaka da jami'ar.