
Hedikwatar tsaron Najeriya ta fara bincike kan labarin da matar wani sojan Najeriya Seaman Abbas Haruna ta bayar na daure mijinta har tsawon shekaru 6.
Matar sojan Seaman Abba ta ce an jefa mijin ta a cikin mummunar ukuba ba tare da gurfanar da shi gaban kuliya ba.
Rundunar sojan karkashin jagorancin shugaban ta Leftanar Janar Christopher Musa ta ce ya zama dole ta gudananar da bincike mai nagarta domin gano gaskiyar lamarin.
Hedikwatar rundunar ta kara da cewa za ta hukunta sojin nata da ya yi wannan aika-aikan matukar ta gano gaskiyar lamarin ba tare da sani ko sabo ba.
Tun ba yau ba ne ake zargin manyan hafsoshin sojan Najeriya da azabtarwa da ma wuce iyaka wajen hukunta kananan sojonin ba tare da fiskantar hukunci ba.
Ko a wannan karon ma rundunar sojan kasar za ta yi amai da lashe kamar lokutan baya ko akasin hakan? lokaci ne kadai zai nuna?