• 17 Jun, 2025

Za Mu Fara Yajin Aiki Watan Disamba—Cewar NLC

Za Mu Fara Yajin Aiki Watan Disamba—Cewar NLC

1000009881.jpg

Kungiyar kwadago a Najeriya ta umarci ma'aikata a jihohin da gwamnatocinsu ba su aiwatar da sabon albashi mafi kankanci na Naira dubu 70 ba su fara yajin aiki daga ranar 1 ga watan Disamba.

Kungiyar ta NLC ta bada umarnin ne a cikin wata takarda bayan wani taro da kungiyar ta gudanar, inda daga bisani shugabanta Joe Ajaero ya fitar da matakin.

Kungiyar ta ce ya zama dole ma'aikata su nuna bacin ransu kan batun da tuni ya zama doka, amma wasu gwamnoni sun ki aiwatarwa.

Takardar ta fito ne bayan taron majalisar zartarwar kungiyar ta NLC da aka yi a birnin Fatakwal da ke jihar Rivers, kudu maso kudancin Najeriya.

A sanarwar, kungiyar ta nuna rashin amincewa da jinkirin da ta ce wasu jihohi a kasar na yi wajen aiwatar da tsarin albashin na 2024, inda ta ce, hakan a matsayin abin da ya saba doka.

Kungiyar ta kara da cewa rashin adalci ne kin aiwatar da tsarin daga wasu gwamnonin kasar.

NLT ta ce, lamarin na kara tsananin wahalar da ma'aikatan kasar ke ciki, yayin da tsadar rayuwa ke kara ta'azzara a fadin Najeriya.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.