• 17 Jun, 2025

Za A Shirya Taron Gudanarda Addua A Najeriya Domin Warware Matsalolin Kasa

Za A Shirya Taron Gudanarda Addua A Najeriya Domin Warware Matsalolin Kasa

1000008047.jpg

Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu da mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu za su jagoranci addu'o'i na musamman domin neman saukin matsalolin Najeriya.

Za a gudanar da addu'o'in ne a karkashin jagorancin shugabannin addinin Musulunci da Kirista domin neman taimakon Ubangiji a kan matsalolin da suka addabi kasar.

Segun Balogun Afolorunikan, wanda shi ne darakta-janar na shirya addu'o'in ne ya furta hakan a birnin tarayya Abuja.

Balogun ya ce akwai bukatar kowa ya bayar da nasa gudunmuwar domin magance matsalolin Najeriya.

Segun ya bayyana cewa akwai bukatar hadin kaiwajen shawo kan dukkan matsalolin kasar kamar yadda aka shirya yin addu'o'i.

Segun ya ce, akwai yakinin Ubangiji zai amsa bukatun kasar ta yadda za a samu sauki don gujewa wahalhalun da ake hasashe kasar za ta shiga a shekara ta 2025 mai zuwa.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.