• 18 Jun, 2025

Za A Fara Amfani Da Iskar Gas A Motoci A Fadin Kasa Baki Daya—Cewar Karamin Ministan Albarkatun Man Najeriya

Za A Fara Amfani Da Iskar Gas A Motoci A Fadin Kasa Baki Daya—Cewar Karamin Ministan Albarkatun Man Najeriya

1000004515.jpg

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bukaci gidajen man fetur a kasar su koma sayarda sabon iskar gas na motoci a fadin kasar.

Karamin ministan albarkatun mai na kasar Ekperikpe Ekpo ne ya furta hakan yayinda ya ke ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zantarwa da aka yi jiya Laraba.

Ministan ya ce, shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa kwamiti kan fara amfani da iskar gas ga masu motoci a fadin Najeriya.

Ekpo ya ce a matsayinsa na ministan albarkatun kasa, yana sanarda yan Najeriya yunkurin gwamnati na fara amfani tukuru da iskar gas a morocin kasar.

Ya ce, iskar gas din a mota ya fi sauki kuma babu cutarda muhalli, yayinda baida hadari ga rayuwar yan kasa kamar man fetur.

Ministan ya bayyana cewar yayinda yan kasar ke sayan litar man fetur Naira 1000, litar gas zai zama Naira 800 ne.

Ekpo ya kara da cewa, za su yi iya kokarinsu domin ganin yan Najeriya da ke birni da kauye sun rungumi sabon tsarin domin sauki da cigaba.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.