
Yan sanda a jihar Kwara arewa masu tsakiyar Najeriya sunyi nasarar kama wani magidanci da laifin satar wayar wutar lantarki.
Bayan an kama mutumin mai suna Idris Hussaini ya ce matsin rayuwa ne ya jefa shi cikin iftila'in satar a birnin Ilorin.
Idris Hussaini ya ce talauci da yunwa ne manyan dalilan da suka sa shi satar wayar wutar.
Hussaini ya saci wayar transfomar a unguwar Oja dake birnin na Ilorin.
Hussaini ce ganin yunwa na kokarin halaka iyalen sa ne ya yanke hukuncin satar wayar wutar.
Yan sandan sun ce sun cafke Idris Hussaini beyan ya yanke wayar daga transfomar wanda hakan ya jefa al'ummar unguwan cikin duhu.