• 18 Jun, 2025

Yawan Yan Najeriya Bai Amfane Su Ba, Domin Abincin Da Talakan Kasar Zai Ci Ya Fi Karfin Sa

Yawan Yan Najeriya Bai Amfane Su Ba, Domin Abincin Da Talakan Kasar Zai Ci Ya Fi Karfin Sa

1000005184.jpg

Duk da cewa yawa na da amfani kuma kariya ne, amma daga dukkan alamu, yawan yan Najeriya bai iya kare su daga wahala ba, domin ba sa iya amfanan yawan nasu ta fannin tattalin arzikin kasa.

Akwai batun tura manyan motoci na buhunan shinkafa ma'aikatun tarayya a farkon wannan makon, domin rabawa talakawa, inda mutane su ka yi ta murna.

A watan da ya gabata ma ministan noma da samarda abinci Abubakar Kyari  ya sanarda fara bada buhunan shinkafan akan Naira 40, 000 kowani buhu a birnin tarayya Abuja.

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta samarda shinkafar ne domin rage radadin yunwa da tsadar abinci da ke addabar yan kasa.

Yanzu haka dai ana sayarda buhun shinkafa akan Naira 80,000 zuwa 100,000 a kasuwa.

A duk kasashen Afrika kamar Rwanda da Afrika ta kudu, sa tallafi a kayayyakin abinci na taimakawa matuka domin hakan na talkafawa masu karamin karfi.

Sai dai duk da ikrarin gwamnatin tarayya na tallafin abincin, buhunan da aka turawa asibiti a Abuja bai isa ba, domin babu tsari da adalci wajen rarraba buhunan shinkafar.

Abin jira a gani dai shi ne ko gwamnatin tarayyar za ta saurari korafin jama'a domin kawo canji wajen raba abincin ko kari kan abinda ke kasa ko akasin hakan.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.