
A yau ne ake sa rai dubban daruruwan yan Najeriya za su fito gudanar da zanga-zangar lumana a fadin kasar.
Zanga-zangar ta zama dole ne a cewar mafi yawancin yan kasar sakamakon talauci da yunwa da ma rashin darajar kudin kasa da talakan Najeriya ke fama da su.
Sauran matsalolin yan kasar da suka tilasta shirin gudanar da zanga-zangar sun hada da cire tallafin mai wanda shi ne ya haddasa tsadar kayayyakin abinci.
Yan Najeriya su ambaci matsalar tsaro da ya addabi yan kasar musamman yankin arewacin kasar, inda kowani wayewan gari sai yan bingiga sun kashe mutane, da matsalar mugun cin hanci da rashawa a kasar.
Yan Najeriya daga jihohin kasar 36 ne za su bazama titunan birane jihohin 36 da ma wasu karin manyan kananan hukumomi domin nuna bacin ransu kan yadda abubuwa ke faruwa.
Tun ba yau ba dai gwamnatin tarayyar Najeriya tayi ta yunkurin ganin ta dakatar da guguwar zanga-zangar da aka shirya tun farkon watan da ya gabata, amma hakan ya ci tura, domin yan kasan sun hau dokin naki.
Gwamnatin kasar ta jibge jami'an tsaro kama daga sojoji zuwa yan sanda da sauran jami'ai masu khaki da ma na cikin farin kaya don kaucewa karya doka da oda daga bata gari yayin zanga-zangar.
Yan Najeriya sun dage cewa yin zanga-zangar yancin su ne kuma hakan zai sa gwamnatin kasr ta yi wani abu don kawo sauyin tsare-tsaren da shugaba Bola Tinubu ya kawo wadanda makiyan talakan Najeriya ne