• 17 Jun, 2025

Yau Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Zai Mika Yaran Da Aka Daure Zuwa Jihohinsu

Yau Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Zai Mika Yaran Da Aka Daure Zuwa Jihohinsu

1000008274.jpg

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai wakilci shugaba Bola Tinubu wajen mika kananan yaran da aka tsare har tsawon watanni uku sakamakon zanga-zangar matsin rayuwa.

Kashim Shettima zai mika yaran ne ga hannun gwamnonin jihohinsu kamar yadda gwamnatin tarayyar ta tsara a jihohin arewacin kasar.

Hakan ya biyo bayan cece-kuce da yan Najeriya da ma kungiyoyin kare hakkin dan'Adam su ka yi, inda suka ce gwamnatin na Bola Tinubu na cin zarafin yara kanan batare da hakkinsu ba.

A yau ne dai kotun tarayya da ke Abuja za ta saki yaran, kana ta mika su hannun mataimakin shugaban kasa Shettima. 

Rahotanni sun nuna cewa ministan Shari'ar kasar Lateef Fagbemi ya kammala duk wani shiri domin sakin yaran zuwa gidajen iyayensu.

A yau ne kuma ake sa ran mataimakin shugaban kasan sanata Kashim Shettima zai mika su zuwa jihohinsu kamar yadda aka tsara.

Yaran dai kanana ne wadanda bisa doka bai kamata a tsare su har tsawon watanni uku ba saboda sun shiga zanga-zangar ne sakamakon masifar yunwa da talauci da gwamnatin Bola Tinubu ta haddasa a cikin al-ummar kasar.
 
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.