
Wani yaro dan shekaru 15 a Najeriya mai suna Master Chinaemere Opara ya yi karar ma'aitakar Ilimi da hukumar shirya jarabawar JAMB da ma Hukumar kula da jami'o'in Najeriya NUC.
Opara ya shigarda karar ne kan sabon tsarin da hukumonin ma'aikatun ilimin suka fitar game da samun gurbin karatu a jami'o'in kasar.
Yaron ya shigar da karar ne babban kotun tarayya da ke babban birnin tarayyar kasar Abuja jiya Litini ta hannun mai kula da lamuransa Mr Maxwrll Opara wanda ke zama mahaifin sa kuma lauyansa.
Opara dai na kalubalantar halaccin sabon tsarin bada gurbin karatun jami'a a kasar da hukumomin ilimi suka fidda, inda ya ce hakan tauye hakkin dan adam ne na samun ilimin jami'a a kasar.
The plaintiff argues that the policy is discriminatory and poses barriers to admission for many prospective students, particularly those from disadvantaged backgrounds.
Yaron ya maida hankali ne kan batun adadin shekaru da hukumomin kula da ilimin suka bijiro da shi, inda dole sai mutum ya kai shekaru 18 kafin ya iya samun damar fara karatun jami'a a kasar.
Opara ya ce, tsarin baya cikin kudin mulkin kasar, don haka baiga dalilin da zai sa hukumomin ilimin za su bijiro da shi ba domin tauyewa yara irinsa zummar shiga jami'a ba.
Yaron ya kara da cewa hakan son kai ne da rashin adalci a cikin wannan zamanin da duniya ta sauya.
Ya kara da cewa cigaba da tilasta sabon tsarin yiwa kundin mulkin sashi 42 na kundin 1999 Act, Cap A9 Vol. 1LFN zagon kasa ne.