
Yara 'yan makaranta 8 sun tsallake rijiya da baya a birnin Lokoja, a jihar Kogi, Arewa maso tsakiyar Najeriya bayan wata babbar motar daukar kaya ta fadi akan motoci.
Hukumar kare hadura ta FRSC a jihar ta ce, babbar motar ta fadi kan kananan motoci amma ba'a samu asarar rayuka ba.
Shufaban hukumar reshen jihar ta Kogi Mista Samuel Oyedeji ne ya tabbatar wa manema labaraifaruwan hadarin misalin karfe 5:30 na yammacin jiya Alhamis.
Hadarin ya faru ne a kasuwar dake birnin Lokoja, inda hadarin ya lalata motocin har guda biyu masu dauke da lambobi kamar haka—Corolla LMA 190AA da Nissan Abuja RSH-241FH.
Ya ce, hadarin ya faru ne bayan an dora ma'dauki wato container a wata babbar mota da aka ajiye a gefen hanya amma ba'a sa sakatar motar ba. Hakan ya sa ma'daukin ya fado kan motocin.
Ma'daukin ya gangara kasa daga cikin motar yayin da motar ke yunkurin hawa wani tudu a kan titi a gefen kasuwar.
Yara daliban suna cikin daya daga cikin motocin, amma Ubanjiji bai bawa ma'daukin ikon danne yaran ba har masu aikin ceto na gaggawa suka je gurin.