
Kungiyar kare hakki da tabbatarda adalci a Najeriya SERAP ta ja hankalin Shugaba Bola Tinubu da ya umurci kamfanin mai na NNPCL a kasar ya soke karin kudin litar mai da ya yi karo na biyu cikin wata daya.
Kungiyar ta ce ya zama dole kamfanin NNPCL ya soke karin har sai kotun tarayya ta yanke hukunci kan shigarda karar da kungiyar ta yi game da karin kudin man.
Kungiyar ta SERAP dai ta yi karar kamfanin mai na NNPCL kotu ne domin sanin ko kamfanin man na da hurumin kara kudin litar man fetur ko akasin haka.
Hakan ya biyo bayan karin kudin litar mai da kamfanin NNPCL ya yi, makon da ya gabata, inda a waje guda gidajen mai na NNPCL ke sayarda man kan farashi daban-daban.
Yayin da gidajen man kamfanin NNPCL da ke birnin tarayya Abuja ke sayarda litar man fetur kan kudi Naira 1,030, wasu gidajen man na kamfanin na sayarda litar man kan kudi Naira 998 bayan karin kudin man.
A wata budaddiyar wasika da mataimakin shugaban kungiyar ta SERAP ya sanyawa hannu, kungiyar ta bayyana cewa karin kudin man da kamfanin NNPCL ya yi tamkar raina kutu ne, domin kungiyar ta shigar da kara kan karin kudin man na watan da ya gabata.