• 18 Jun, 2025

'Yan Ta'adda Sun Hallaka Dalibai A Jihar Yobe

'Yan Ta'adda Sun Hallaka Dalibai A Jihar Yobe

gettyimages-1241732420-612x612-1.jpg

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun hallaka daliban makarantar Sakandare a garin Geidam a jihar Yobe, arewa maso gabacin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa makasan sun shiga Hausari Qaurters da ke garin na Geidam misalin karfe 3:44 na safiyar yau Juma'a yayin da wadanda aka kashe ke bacci.

'Yan bindigan sun tashi daliban daga bacci suka fidda su waje daga bisani suka harbe su daya-bayan-daya har lahira, yayinda wani dalibi guda ya samu raunin alburushi lokacin da yayi kokarin tserewa maharan.

Yanzu haka dai mutanen garin na Geidam na zaman dar-dar sakamakon faruwar iftila'in da yayi sanadin rayuka.

Mai magana da yawun rundunar 'yansandan jihar Yobe DSP Dungus Abdulkarim ya tabbatar da faruwan lamarin.

A nashi bangaren, mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya ta Operation Lafiya Dole runduna ta biyu da ke jihar Yobe ya ce nan ba da dadewa ba za su fitar da cikakken bayani kan harin rashin imani.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.