• 18 Jun, 2025

'Yan Siyasa Na Amfani Da Na'urar Gano Mafakar Masu Garkuwa Domin Ceto Iyalen Su Da 'Yan'matan Su Kadai

'Yan Siyasa Na Amfani Da Na'urar Gano Mafakar Masu Garkuwa Domin Ceto Iyalen Su Da 'Yan'matan Su Kadai

screenshot-20240831-085819-1725091131520.jpg

Wani babban jami'in 'yansandan Najeriya mai ritaya ya zargi masu mulki da nuna sonkai wajen tunkarar matsalar garkuwa da mutane a kasar.

Dan'sandan ya ce mafi yawancin 'yan siyasa na amfani da na'urar gano inda ake garkuwa da iyalensu da 'yan uwan su da ma 'yan matan su, yayin da sauran talakawa basuda gatan hakan.

Jami'in ya ce abin takaici ne shugabanni su rika nuna halin rashin imani ga talakawan da suka zabe su.

Jami'in wanda tsohon dansandan Najeriya ne ya bayyana cewa an tanadi na'urar ne domin gano duk inda a ke garkuwa da dan kasa batare da nuna bambanci ba, amma akasin hakane ke faruwa a kasar.

Ya kara da cewa na'urar na da matukar amfani domin ta na gano inda wanda aka yi garkuwa da shi ya ke da ma wadanda suke garkuwar tare da nade muryoyin duk zantukan da masu garkuwar suka yi.

Jami'in ya ce wani karin abin haushi shi ne da manyan sufetocin 'yansandan kasar da suka gabata aka yi amfani domin sunada masaniyar abin da 'yan siyasa ke yi.

Jami'in ya ce karuwar tabarbarewar tsaro a Najeriya ne ya tilasta shi furta rashin adalcin da shugabanni ke wa al'ummar kasar, wanda hakan babban barazana ce ga harkar tsaro.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.