• 18 Jun, 2025

'Yan Siyasa A Yau Sun Zabi Tara Dukiya Ba Aiki Wa 'Yan Kasa Ba—Cewar Tsohon Ministan Abuja

'Yan Siyasa A Yau Sun Zabi Tara Dukiya Ba Aiki Wa 'Yan Kasa Ba—Cewar Tsohon Ministan Abuja

1000005175.jpg

Tsohon ministan birnin tarayyan Najeriya  Mohammed Abba Gana ya ce hakkin da ya rataya kan yan siyasa shi ne yi wa kasa da yan kasa aiki ba tara dukiya ba.

Mohammed Gana ya furta hakan ne yayinda ya ke bayyana yadda su ka yi aikin ofis a baya, inda ya ce, har yanzu bai mallaki gidan kansa a Abuja ko jiharsa ta Borno ba.

Mohammed Gana mai shekaru 81 kuma tsohon kwamishina a jihar Borno  ya  ce, ya yi kokarin tsayawa takarar gwamna a jihar sa a shekar ta 1979 karkashin jam'iyyar GNPP domin bada gudumawarsa amma hakan bai yiwu ba.

Gana ya bayyana cewa a shekara ta 2001 ne aka bashi ministan Abuja lokacin mulkin Olusegun Obasanjo, inda daga nan ya yi ritaya daga siyasar kasar.

Mohammed Gana ya karanci ilimin fasahar wutar lantarki ne a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria jihar Kaduna.

An haifi Mohammed Gana ne a shekarar 1943 a garin Damboa da ke kudancin jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.

Gana ya ce sun shiga siyasa ne domin bautawa al-umma, amma abin takaici yan siyasa a yau suns shiganta ne don su azurta kansu. Sun maida siyasa sana'a.

Gana ya kara da cewa babu wanda ya mallaki wata dukiya a wancan lokaci. Tunaninsu kullum shi ne cigaban yan Najeriya ba tara dukiya ba.

Mohammed Gana ya ce baida gida mallakar sa ko a Maiduguri jiharsa ballantana a birnin tarayya Abuja.

Mohammed Gana ya kara da cewa, gida daya ya mallaka wadda ya gina da kudin rance da ya karba a bankin lamuni na tarayya.

Bayan haka, Gana ya ce, fili guda daya kadai ya mallaka a Abuja kuma bai gina ba har yabar ofis saboda baida kudin gina wa.

A karshe bayan ya bar kujerar ministan Abuja, mutumin da ya hau kujerar bayan ya sauka, ya kwace  filin a hannunsa. Duk da cewa yanada takardar mallakar filin, amma ministan ya soke.

Mohammed Gana ya kara da cewa, yanzu haka gidan da yake zaune a Abuja ba nashi ba ne, wani bawan Allah ne ya bashi gidan shekaru 5 da suka gabata, batare da yana biyan kudin hayaba kuma ba kyauta ba.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.