• 18 Jun, 2025

'Yan Shia A Najeriya Sun Yi Karar Rundunar 'Yansandan Kasar

'Yan Shia A Najeriya Sun Yi Karar Rundunar 'Yansandan Kasar

img-7475.jpeg

Mabiya darikar Shia a Najeriya sun mika wa kungiyar tarayyar Turai da kungiyar kare hakkin bil'adama korafe-korafen su kan cin zarafin su da jami'an 'yansandan Najeriya ke yi.

Kungiyar sun nuna fusatar su kan yadda 'yansandan Najeriya ke amfani da karfi wajen cire wa matan su hijabi da batanci ga addinin Musulunci a bainar jama'a.

A ranar 4 ga wannan watan ne kungiyar suka aika korafin a wata takarda da wakiliyar kungiyar Fatima Aliyu ta sanya wa hannu.

Kungiyar sun bukaci ayi amfani da na'urorin zamani wajen binciken cin zarafin da 'yansandan babban birnin kasar Abuja su ka yi wa 'ya'yan kungiyar ranar 26 ga watan Agustan da ya gabata wanda aka tura bidiyon a yanar gizo.

'Yan Shian suna zargin babban sufeton 'yansandan kasar Kayode Egbetokun da kwamishinan 'yansandan birnin tarayya Abuja Benneth Igweh da jagorantar cin zarafin da ake musu.

'Yan Shian kana sun mika korafin su kan kama 'yan'uwan su da jami'an 'yansandan Abujan sukayi yayin da suke tattakin Arba'een kamar yadda suka saba cikin lumana da sauran cin zarafi da wulakanta addinin Islama da 'yansandan ke musu.

Kungiyar ta mabiya Shia sun ce matukar ba a dauki mataki kan cin zarafi da batanci ga addinin Musulunci da jami'an 'yansanda ke musu ba, hakan zai kawo tarzoma a kasar, domin ba za su ci gaba da lamunta ba.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.