
Yan sanda a Abujan Najeriya sun harba barkonon tsohuwa a kan daruruwan masu zanga-zangar lumana a dandalin mikiya a birnin tarayyar.
Masu zanga-zangar sun hallara ne a dandalin na Eagle inda jami'an tsaro suka harba musu barkon da zummar watsa su.
Wani dan jarida mai aiki da gidan talabijin na News Central Television na daga cikin wadanda gongonin barkonon tsohuwar ya buge su yayin da yake gudanar da aikin sa.
Kwamishinan yan sandan birnin tarayyar Benneth Igweh ne ya jagoranci cin zarafin masu zanga-zangar lumana tare da tauye hakkin yan jarida na gudanar da ayyukan su cikin yanci da walwala.
Tun farko dai ministan Abujan Nyesom Wike yayi alwashin bazai kyale wani ya gudanar da zanza-zanga a dandalin Eagle ba sai dai filin wasan kwallo na MKO Abiola.