
Yan sanda sun cafke mai unguwar Tambai a Jihar Katsina arewa maso yammacin Nijeriya.
An kama mai unguwan ne bisa zargin bayar da bayanan mutane ga yan bindiga da suka addabi jihar da ma yankin bakin baki daya.
Mai unguwar ya bayyana cewar kafin ya shiga hannu, sau biyu yana bayar da bayanan wasu mutane da ke unguwarsa.
Mai unguwar ya kara da cewa sakamakon bayar da bayanan mutanen da ya yi, maharan sunyi nasarar sace su da na karbar kudaden fansa amma ko sisi ba su bashi ba.
Tun ba yau ba ne dai masu bawa yan bindiga bayanai ke korafin basa samun wani abin kirki daga hannun yan bindigan.