
Bankin Duniya ya fitarda wani kididdiga inda ke nuna kasashe masu karamin karfi a duniya ka iya shafe shekaru 100 nan gaba ba su iya kawo karshen talauci tsakanin al-ummomin su ba.
Bankin Duniyan ya ce Najeriya na daga cikin kasashen da za su ci gaba da fiskantar mummunan talauci a duniya kafin ta kawo karshen matsalar.
Bankin duniyan ya ce duk lokacin da mutum baya iya samun kudin shiga da ta kai Dala 6.85 a rana yana cikin talauci, wanda mafi yawancin yan kasashen ciki harda Najeriya ke fama.
Wani masanin tattalin arziki wanda shi ne mataimakin shugaban bankin duniya kan ci gaban tattalin arziki Indermit Gill ne ya furta haka.
Gill ya ce, akwai bukatar kasashen su sa jari mai karfi a harkokin kiwon lafiya da ilimi da rage talauci domin kawo sauyi.
A daya bangaren kuma, Hukumar Lamuni ta duniya wato IMF ta tabbatar da cewa yawan basuka na daya daga cikin dalilan da za su ci gaba da sanya Najeriya cikin matsalolin tattalin arziki.