• 17 Jun, 2025

Yan Najeriya Sun Fara Ajiye Motoci A Abuja, Yayinda Wasu Suka Fara Tafiya A Kasa Sakamakon Karin Kudin Mai Karo Na 3 Kasa Da Watanni Biyu

Yan Najeriya Sun Fara Ajiye Motoci A Abuja, Yayinda Wasu Suka Fara Tafiya A Kasa Sakamakon Karin Kudin Mai Karo Na 3 Kasa Da Watanni Biyu

1000006541.jpg

Yan Najeriya Sun fara nesantar gidajen mai a yan kwanakin nan tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sake kara farashin man fetur.

Lamarin ya janyo wa yan kasar da dama wahalhalu musamman marasa karfi,  kuma masu ababen hawa suka fara ajiye motocinsu saboda tsadar man.

A jiya Talata ma yan Najeriya sun wayi gari da sabon farashin man, inda ya koma N1,050 zuwa 1,060 a gidajen mai na kamfanin NNPCL mallakar gwamnatin ƙasar.

Yanzu dai da yawan mutane sun gwammace su hau motocin haya wajen yin zirga-zirga maimakon amfani da motocinsu, inda wasu ma suka gwammace takawa da ƙafa zuwa wuraren aiki ko kasuwancisu.

Hanyoyi da aka saba ganin cunskoso a baya a wasu birane sun kasance babu mutane a yanzu, musamman a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Akwai wasu rahotanni da ke cewa wasu mutane sun koma sayar da motocinsu domin maye gurbinsu da wadanda ba su shan mai sosai.

Yayin da karin farashin man fetur ɗin ke ci gaba da zama kamar wasan yara a fadin Najeriya, masu gidajen na kokawa game da rashin zuwan masu saye.

Sun ce yanzu abin da suke sayarwa bai taka kara ya karya ba, idan aka kwatanta da baya, lamarin ya sa wasu yankasuwa na barazanar rufe gidajen man nasu.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.