
Mai magana da yawun shugaban kasan Najeriya Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu na sane da wahalhalun da yan kasa ke cikin a kowani lokaci.
Onanuga ya ce, sabanin yadda wasu bata gari ke kiran shugaban kasar da suna "T-Pain, shugaban na aiki tukuru don kawo saukicikin rayuwar yan Najeriya.
Onanuga ya kara da cewa abubuwa za su daidaita nan ba da jimawa ba domin shugaba Tinubu ba ya bacci saboda matsalolin Najeriya da halinda yan Najeriya ke ciki.
Mai magana da yawun shugaban ya furta haka ne yayida ya ke amsa tambayoyi a tashar talabijin na Channels cikin shirin siyasa a ranar Lahadi.
Onanuga ya ce shugaban kasa bai hau karagar mulkin Najeriya don ya jefa yan kasa cikin wahala ba, sai dai don ya kawo canjin lamura musamman a tattalin arzikin kasar.
Onanuga ya kara da cewa, shugaba Tinubu baisan yan Najeriya na kiransa da lakabin suna "T-Pain ba.
Bayo Onanuga ya ce a kullum shugaba Tinubu na jin radadin da yan Najeriya ke ji sakamakon matsin tattalin arzikin kasa da ya shafi kowa, kuma yana iya kokarinsa domin kawo karshen lamarin.