• 17 Jun, 2025

'Yan Najeriya Na Cikin Matsin Tattalin Arziki—Cewar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo

'Yan Najeriya Na Cikin Matsin Tattalin Arziki—Cewar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osibanjo

1000009171.jpg


Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya shawarci Shugaban kasa Bola Tinubu ya maida hankali wajen kyautata rayuwar 'yan Najeriya da ke fama da wahalhalu.

Osinbajo ya furta haka ne a wajen wani taro, inda ya ce, akwai bukatar ceto 'yan kasa daga matsin talauci da su ke fama da ita cikin gaggawa.

Yemi Osinbajo ya ce, ya kamata Shugaba Bola Tinubu ya maida hankali wajen.kawo saukin kayayyakin abinci da kiwon kafiya da sufuri da matsugunni da 'yan Najeriya ke fama da tsadarsu.

Farfesa Osinbajo ya kara da cewa tsadar abubuwan more rayuwa na shafar 'yan kasar musamman kananan yara wadanda ya kamata a basu kolawa ta musamman.

Osibanjo ya ce, sama da mata kashi 67 ne musamman a arewacin kasar ke fama da rashin ilimi, wanda hakan ke shafar rayuwarsu.

Osibanjo ya ce, duk kasar da rabin al-ummarta ke fama da rashin ilimi, wannan kasar ba za ta ci gaba ba kodan idan gwamnati ba ta yi wani abu akai ba.

Farfesa ya ce, akwai bukatar gwamnatin Bola Tinubu ta shiga cikin lamuran 'yan Najeriya domin kawo sauki ta hanyar ilmantarwa da karfafa tattalin arzikinsu.

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.