• 17 Jun, 2025

'Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Tsokaci Kan Kunnen Uwar Shegu Da Shugaba Tinubu Ya Yi Kan Kudurin Harajin VAT

'Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Tsokaci Kan Kunnen Uwar Shegu Da Shugaba Tinubu Ya Yi Kan Kudurin Harajin VAT

1000006891-1.jpg

Yan Najeriya na ci gaba da tsokacin dangane da taurin kai da Shugaba Bola Tinubu ya nuna kan sabon kudurin  kasafin harajin VAT da ya aika majalisar dokokin kasa.

Shugaba Tinubu ya ki amincewa da hukuncin da majalisar zantarwar kasar wadda mataimakinsa Kashim Shettima ke jagoranta, inda suka shawarci shugaban ya janye niyyar tasa.

Da farko dai gwamnonin arewacin kasar ne suka yi fatali da kudurin sabon tsarin harajin bayan sun gudanarda wani taro a birnin Kaduna, inda suka ce sabon tsarin zagon kasa ne ga yankin mai jihohi 19.

Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya ce, shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar ce ke da hurumin amincewa da sabon kudurin ba wasu ba.

Shugaba Tinubu ya yi kunnen uwar shegu da shawarar da aka bashi na janye kudurin daga majalisar dokokin har sai majalisar sun yanke nasu hukuncin.

An dau matsayar kin amincewa da kudurin Bola Tinubu ne bayan taron da masu ruwa da tsaki sukayi a kasar wanda ya hada da gwamnonin kasar 36 da mataimakin shugaban kasa wanda ya jagoranci zaman.

An gudanarda zaman ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis domin duba lamarin, amma a karshe gwamnonin kasar musamman na yankin arewaci sunyi watsi da batun karo na biyu.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya bayyana cewa sunyi watsi da sabon tsarin harajin na VAT ne domin ba alkairi ba ne ga Najeriya.

Gwamnonin arewa sun ce sabon tsarin tattara harajin na VAT da shugaba Bola Tinubu ya aika majalisar dokokin kasar ya nuna zagon kasa karara ga yankin arewa wanda ke da dunbun al-umma da albarkatun noma.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.