
Yan Najeriya na ci gaba da yin Allah wadai da karin kudin litar man petur a kasar daga Naira 897 zuwa Naira 10,03 a gidajen man gwamnati na NNPCL, yayinda gidajen man yan kasuwa su ka fara sayarwa Naira 1,400 zuwa 1,500.
A baya yan kasar sunyi ta fatan litar man petur zai yi sauki ta yadda talaka zai iya saya ba tare da takura ko matsi ba sakamakon gina matatar mai da Dangote ya yi.
A yanzu dai ya tabbata talakan Najeriya bazai samu wani sauki ba ta fannin farashin man petur a kasar duk da matatar Aliko Dangote ta fara aikin tacewa da sayar da man.
Yan kasar dai da ma masana tattalin arzikin sun nuna damuwa kan rashin jagoranci na adalci daga shugabannin Najeriya.
A zahiri dai man petur ana tace shi a cikin gida ne, inda babu biyan kudin dakon sa daga kasashen ketare da ma sauran kudade da ake biya don shigowa da tataccen man kamar yadda aka saba a baya amma saukin man ya gagara wanzuwa.
Abin tambaya shi ne menene dalilin da ya sa kamfanin mai na NNPCL ya kara kudin litar man a gidajen mai na gwamnati har sau biyu kasa da wata daya kacal bayan an fara tace man a cikin gida?
Su waye ke da alhakin kara kudin man petur ko akasin haka a kasar tunda yanzu yan kasuwa ne ke tace danyen man kuma a cikin gida?
Wadannan da ma wasu tambayoyi yan Najeriya ke dauke da su tun karin man na farko zuwa wanda aka yi jiya.