• 18 Jun, 2025

'Yan Majalisar Wakilan Najeriya Sunyi Watsi Da Bukatar Shugaba Tinubu Kan Karin Kudin Haraji A Kasar

'Yan Majalisar Wakilan Najeriya Sunyi Watsi Da Bukatar Shugaba Tinubu Kan Karin Kudin Haraji A Kasar

1000001483.jpg

Akwai yiwuwar rigima tsakanin fadar shugaban kasa da majalisar wakilan Najeriya bayan yan majalisar sun yi watsi da kokarin shugaba Tinubu na fadada karbar haraji daga hannun yan kasar.

Fadar shugaban kasar dai na yunkurin karin haraji kan talakan kasar bayan halin matsin tattalin arziki da tuni suke  ciki.

Wannan ya biyo bayan wata muhawara da aka tafka a zauren majalisa tsakanin yan majalisar wakilan sakamakon gabatar da wani kuduri da aka yi wa karatun farko da ke neman karin haraji kan yan kasar bayan wadanda ke kansu.

Majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da yunkurin nata domin babu wani dalilin da ya zama farilla da zai sa yin hakan.

Majalisar wakilan ta kara da cewa  tattalin arzikin kasar a halin da ake ciki yanzu ba ya taimakon yan Najeriya face talauci da yunwa da tsadar rayuwa da ma rashin aikin yi tsakanin matasar kasar.

Shugaban marasa rinjayi a majalisar Ali Sani Madakin Gini na daya daga cikin masu  adawa da matakin na gwamnatin tarayya inda ya ce talakawan kasar na cikin mawuyacin hali.

Ali Madaki ya kara da cewa duk wani yunkurin kara wa talakan Najeriya haraji zai kara jefa shi ne cikin karin masifar tattalin arziki.

Fadar shugaban kasar Najeriya dai na da niyyar fadada hanyoyin kudin shiga ne ta hanyar tilasta yan kasar biyan haraji a fannonin da basa tsammani.

Abin jira a gani daibshi ne yadda za ta kaya tsakanin majalisar wakilan da shugaba Bola Tinubu kan wannan yunkurin na shi.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.