• 18 Jun, 2025

'Yan Kungiyar Boko Haram Sun Hallaka Mutane A Jihar Yobe

'Yan Kungiyar Boko Haram Sun Hallaka Mutane A Jihar Yobe

fb-img-17252680183686238.jpg


'Yan kungiyar Boko Haram sun kai wani hari a kauyen Mafa da ke Karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe, arewa maso gabacin Najeriya.

'Yan ta'addan sun hallaka mutanen da ba a san adadin su ba, inda suka kona gidaje da dama da ababen hawa.

Mai magana da yawun rundunar 'yansandan jihar Yobe Dungus Abdulkarim ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na NAN a birnin Damaturu.

Dungus ya ce maharan sun kai farmakin ne jiya Lahadi misalin karfe 4 na yamma a kauyen Mafa kamar yadda ofishin su na yankin ya tabbatar musu.

'Yan Boko Haram din sun harba makami mai linzami mai suna RPG da dama  inda sama da babura 50 suka kone kurmus bayan kona gidaje da kashe mutane.

A makon da ya gabata ne wasu 'yan bindigan suka kai hari wani makarantan Islamiyya a garin Geidam duka a jihar ta Yobe inda anan ma aka rasa rayuka.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.