• 17 Jun, 2025

'Yan Gudun Hijira A Jihar Borno Sun Bayyana Mawuyacin Hali Da Su Ke Ciki

'Yan Gudun Hijira A Jihar Borno Sun Bayyana Mawuyacin Hali Da Su Ke Ciki

1000009696.jpg

'Yan gudun hijira a jihar Borno, arewa maso gabacin Najeriya sun ce gwamna Babagana Umara Zulum ya gaza cika alkawarin da ya yi musu na maida su  matsuguninsu.

'Yan gudun hijiran wadanda asalin 'yan yankin Konduga ne sun ce har yanzu gwamna bai cika alkawarin maida su matsugunninsu da ke garin Konduga ba kamar yadda ya yi alkawari.

Wani mai suna Malum Amsami ya ce, Gwamna Zulum dai ya yi wa yan gudun hijiran alkawari zai maida su garinsu na Konduga a lokacinda ya ke yakin neman zaben gwamnan jihar ta Borno.

'Yan gudun hijiran dai sun tsere daga Konduga ne sakamakon hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram a yankunansu.

Mafi yawancin 'yan gudun hijiran dai na tsugune ne a sansanonin yan gudun hijira da ke birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Sun ce wasu daga cikinsu na tare da danginsu a birnin Maiduguri, yayinda sauran ke zaune a sansanin yan gudun hijira da ba na gwamnati ba, bayan an rufe sansanin gwamnati tun karshen watan Disamban shekarar 2021.

Amsami ya ce, akwai bayanan da su ka nuna cewa gwamnatin jihar ta Borno ta maida wasu yan gudun hijiran yan garin Kayamla zuwa gida, amma su har yanzu ba su san matsayinsu ba.

'Yan gudun hijiran sun bayyana cewa sun rabu da garinsu tsawon shekaru 10 kenan yau amma ba su da wani kwarin gwiwar komawa gida.

Sun bayyana cewa su na cikin mawuyacin hali na rashin matsuguni mai nagarta, yayinda su ke fama da rashin abinci da ruwa da magunguna da sauran ababen rayuwa.

'Yan Kondugan sun ce, kafin masifar 'yan Kungiyar ta Boko Haram, suna rayuwa cikin annashuwa da wadata, inda su ke noma da sana'o'insu, amma a yanzu sun rasa komai.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.