• 18 Jun, 2025

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutum 10 A Wata Kauye A Jihar Zamfara

Yan Bindiga Sun Yi  Garkuwa Da Mutum 10 A Wata Kauye A Jihar Zamfara

fb-img-17238022758435079.jpg

An sace a kalla mutum 10 a kauyen Matusgi da ke karamar hukumar Talata Mafara a jihar Zamfara arewa maso yammacin Najeriya.

An sace mutanen ne bayan wasu yan bindiga sun shiga kauyen misalin karfe 2 na daren yau Juma'a da manyan makamai.

Yan bindigan sunyi ta harbe-harben kan mai uwa da wabi kafin daga bisani sukayi nasarar arcewa da mutum goma.

Duk da cewa ba a samu rahotannin rasa rai ko daya tilo ba, yan bindigan sun jefa yan kauyen cikin jimamin rashin yan uwansu.

Daga cikin wadanda yan bindigan suka dauka har da wani mara lafiya da ke kwance a asibiti tare da ledan ruwa a jikin sa da ma wata mata.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.