
Sama da mutum 150 ne akayi garkuwa da su a wani sabon hari da 'yan bindiga suka kai kauyukan Gobir da ke jihar Sokoto arewa maso yammacin Najeriya.
'Yan bindigan sun kuma sace shanu sama da guda 1000 yayin hare-haren da suka kaddamar kan al'ummar yankunan.
'Yan ta'addan sun kai hare-haren ne kwanaki kadan bayan kashe sarkin na Gobir Alhaji Isa Muhammad Bawa bayan sunyi garkuwa da shi.
Farfesa Bello Bada na tsangayar koyon harshen Turanci a jami'ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato ya tabbatar da hare-haren, inda ya ce abin takaici ne dawowar 'yan bindigan kwanaki kadan bayan sun hallaka sarkin Gobir.
Farfeasa Bello ya kara da cewa akwai zarge-zargen cewa wasu mutane daga cikin al'ummar Gobir da kewaye na da hannu a cikin ta'addancin da ke faruwa, domin suna zance da 'yan bindigan ta wayar salula.