• 17 Jun, 2025

Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'in Fasa Kwauri

Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'in Fasa Kwauri

Yan Bindiga Sun Hallaka Jami'in Fasa Kwauri

img-20220729-wa0024.jpg

Yan bindiga sun hallaka wani babban jami'in kula da fasa kwauri a yankin Koko dake jihar Kebbi, arewa maso yammacin Najeriya.

Yan bindigan a lokaci guda sunyi garkuwa  da wani jami'in a wani hari da yan bindigan suka kai yayin da jami'an ke ziga-zirgar aiki.

Mai magana da yawun hukumar ta fasa kwauri shiyyar jihar ta Kebbi Mohammed Tajuddeen Salisu ne ya bayyana hakan a birnin Kebbi.

Tajuddeen ya kara da cewa yan bindiga sun bukaci kudin fansa bayan sun kama jami'in nasu yayin da suka kaske Dabo Umar.

Tajuddeen yace, a yanzu haka babban jami'in Babagana Abba Kabiru yana hannun yan bindigan.

Muhammed Tajuddeen yace sun kai gawar jami'in nasu Dabo Umar da yan bindigan suka kashe Kaduna domin binne shi.

 

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.