
Gwamnatin jihar Legas ta ce yin bahaya barkate a filaye da titunan jihar ya kwace fili kusan kilomita 7.8 a titin legas zuwa jihar Ogun kadai.
Babban manaja hukumar jiha ta LADEPA Babatunde Ajayi ne ya furta haka yayin tattaunawa da manema labarai a birnin na Eko.
Ajayi ya bayyana hakan a wajen wani taro mai taken gina jihar Legas mai dorewa cikin jajircewa.
Babatunde Ajayi ya ce yin bahaya barkate kan tituna na daya daga cikin manyan matsaloli da jihar ke fama da su, inda ya ce sun dukufa wajen ganin sun kawo karshen matsalar.
Ajayi ya kara da cewa abin takaici ne kasancewar Legas birni ce mai yawan jama'a amma cikin mutane ake yin bahaya.
Babatunde Ajayi ya ce tuni sun hada gwiwa da jihar ta Ogun domin kawo karshen matsalar.