
Talauci da rashin tsaro har ma da rashin rayuwa mai inganci sun tilasta yan Najeriya da dama barin garuruwan su zuwa birnin tarayya Abuja.
Yan kasar suna barin garuruwa da kauyukan su daga mazauna yankin kudancin kasar zuwa yan arewaci domin zuwa Abuja da zummar inganta rayuwar su.
Yan kasar da dama da suka je Abuja na zama a tsoffin motoci da aka bar amfani da su da gidajen da ba a karasa su ba, bayan sun iske rayuwar ba yadda sukayi tsammani ba a birnin tarayyar.
Kyau da arziki da ma sauran abubuwa masu jan hankali ne ke tunzura yan kasar tunanin zama a birnin Abuja. Amma daga karshe idan su ka je, labarin na canja wa.
Najeriya dai kasa ce mai dunbun arziki a kaf nahiyar Afrika, amma har yanzu talakawan kasar na fama da yunwa da mummunar talauci da rashin tsaro sakamakon rashin shugabanci mai nagarta.