• 17 Jun, 2025

Yadda Saurayi Da Budurwa Su Ka Yi Garkuwa Da Wata Mata 'Yar Shekaru 70

Yadda Saurayi Da Budurwa Su Ka Yi Garkuwa Da Wata Mata 'Yar Shekaru 70

1000012351.jpg

Rundunar 'yansandan Najeriya a Jihar Enugu ta cafke saurayi da budurwarsa kan zargin hannu a garkuwa tare da hallaka wata mata 'yar shekara 70 mai suna Mary Nwatu.

Ana zargin mutanen biyu da binne marigayiyar bayan sun kashe ta a watan Satumban wannan shekara, watanni biyu kenan da su ka gabata.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar Daniel Ndukwe ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a birnin Enugu, kudu maso gabashin Najeriya.

Sanarwan ta bayyana sunayen mutanen Ikechukwu Okoye mai shekaru 33 da budurwarsa Juliet Ogbodo.

Dukkan wadanda ake zargi da aika-aikar yan gari daya ne, wato garin Onuorie-Obuno da ke yankin Akpugo a karamar hukumar Nkanu West da ke jihar Enugu.

Ndukwe ya bayyana cewa ranar 15 ga watan Satumba ne matar ta bace, inda aka neme ta aka rasa, yayinda ta ke hannun 'yan ta'addan.

Ikechukwu Okoye wanda shi ne jagora ya ce, sun fara neman kudin fansa miliyon 6 ne daga hannun 'ya'yan marigayiyar ranar 5 ga watan Oktoba.

Ikechukwu Okoye ya amsa laifinsa na hallaka matan, tare da neman kudin fansa, inda ya ce, ya rage zuwa miliyan 3, amma a karshe ya karbi Naira dubu 20.

 

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.