• 18 Jun, 2025

Yadda Mawakan Masana'antar Kannywood Ke Samun Kudaden Shiga

Yadda Mawakan Masana'antar Kannywood Ke Samun Kudaden Shiga

1000001780.jpg

Mawakan  masana'antar  Kannywood da dama sun fara kwasar ribar  sanadiyar dora wakokisu a  runbun bidiyo  ta YouTube.

YouTube dai wata kafa  ce  da take bawa manya da kananan mawaka damar nuna fasaharsu cikin sauki.

Yawancin mawakan Hausa sun samu daukaka ne a sanadiyar sanya wakokinsu a gidajen rediyo da tarukan bukukuwa da suke halarta.

Da dama daga cikin mawakan Hausa na zamani sun samu daukaka ne a sanadiyar wakokin fina-finai da suke yi, inda a zamanin baya jaruman da suka hau wakokin suka shahara sama da mamallaka wakokin.

Daga baya mawakan Kannywood sun fara shirya albam na wakokii a fai-fayin CD suna sayarwa kamar yadda ake yin fina-finai.

Wannan tsarin shi ma  ya kawo sauyi a bangaren wakokin Hausa a masana'antar ta Kannywood.

Mawaka irin su Abubakar Sani da Adam A. Zango da Sadi Sidi Sharifai da Nazifi Asnanics ne suka shige gaba a wannan zamanin, inda wakokinsu suka ci kasuwa sosai, kuma suka kara samun daukaka bayan an dade ana jin muryoyinsu a fina-finai.

Amma a yanzu zamani ya sauya, inda mawakan Hausa da dama suna sabunta salon fitar da wakokinsu ne ta hanyar dorasu a YouTube suna samun kudi.

Wannan lamarin ya fitar da sababbin mawaka da sosai a yanzu cikin masana'antar ta Kannywood.

Wasu daga cikin mawakan da sanadiyar YouTube suka samu daukaka sun hada da Hamisu Breaker da Umar M Sherrif da Ali Jita da G-Boy da Ado Gwamnja da sauransu.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.