
A baya dai shugabannin APC ciki har da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun fito kan tituna kasar domin nuna adawar su da kokarin cire tallafin man petur da Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi a wancan lokacin.
Tsohon Shugaban kasa Buhari dai shi ne ya jagoranci zanga-zangar ta kwanaki. Akwai tsohon shugaban jam'iyyar ta APC Oyegun da mataimakin sakataren APC wanda yanzu haka Gwamnan jihar Yobe ne Mai Mala Buni.
Akwai kuma sakataren jam'iyyar ta APC kuma tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa'i. Dukkan su jiga-jigai ne yau a jam'iyyar APC mai mulki da ta cire tallafin mai duk da cewa sun kyamacin batu.
Abin tambaya anan shi ne? shin dama wadannan mutanen ba don talakan Najeriya sukayi adawa da cire tallafin man petur ba ne?
Idan kuma don talakawa sukayi meyasa yanzu sukayi shiru?