• 17 Jun, 2025

Yadda Dangantaka Ta Yi Tsami Tsakanin Gwamnan Kano Abba Da Kwankwaso

Yadda Dangantaka Ta Yi Tsami Tsakanin Gwamnan Kano Abba Da Kwankwaso

1000008720.jpg

Dan majalisar tarayya mai wakiltan Dala a jihar Kano Aliyu Sani Madakin-Gini ya zargi gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da yiwa jagoran jam'iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso rashin da'a.

Madaki ya bayyana cewa hakan ya samu asali ne tun daga batun kwangilar magunguna da tsarin tallafin karatu kyauta na jihar ta Kano.

Aliyu Sani Madakin-Gini wanda ya sanarda ficewarsa daga tafiyar Kwankwasiyya ya ce, ya komawani bangaren jam'iyyar ta NNPP.

Yayinda yake yiwa magoya bayansa jawabi a wani bidiyo ya ce, Kwankwaso mutum ne mai son biyayya dari-bisa-dari, inda ya ce, Kwankwaso na son ya juya dukkan kananan hukumomin jihar Kano 44 yadda yake so.

Madaki ya bayyana cewa Kwankwaso baiji dadin abinda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ba, inda gwamna ya bada umarnin bincike kan badakalar kudaden bada tallafin karatu kyauta a jihar, wanda hakan ka iya shafar mulkin Kwankwaso domin a lokacin ne aka fara bada kwangilar tallafin karatun.

Bincike ya nuna, a cewar Aliyu Sani Madakin-Gini, mutum 400 ne kacal aka bawa tallafin zuwa karatu kasashen waje cikin mutum 1,001 da aka ware kudaden turasu karatun.

Madaki ya ce, yanzu haka rashin fahimta tsakanin gwamna Abba Kabir Yusuf da Rabiu Musa Kwankwaso ya yi tsamari, inda babban Sakataren jihar da Kwamishinan sufuri ke bayan gwamna Abba, wanda a sakamakon haka ne aka dakatar da su daga kujerunsu kwanakin baya.
 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.