
Wata Dalibar jami'ar tarayya da ke jihar Ekiti ta lashe jarabawarta bayan wani malami mai suna Anthony Agbegbedia ya ce ta fadi jarabawar.
Hakan ya biyo bayan bawa wani malami daga wata jami'a pepanta ne domin ya duba, inda a karshe dalibar ta lashe jarabawar.
Rahotanni sun nuna cewa Agbegbedia ya nemi yin lakata da dalibar ne amma ta ki amincewa da bukatarsa, sakamakon haka, ya bata faduwa a jarabawar.
Dalibar da ke shekarar karshe a tsangayar ilimin wanzarda zaman lafiya da warware rekici a jami'ar garin Oye-Ekiki ta ci jarabaawar malamin amma ya kayar da ita saboda neman yin iskanci da ita.
Labarin ya bayyana ne bayan dalibar ta sanarda kafar yada labarai ta Sahara Reporters halin da take ciki.
A yanzu dai an bawa tsangayar umarnin dora sabon sakamakon jarabawar dalibar a kundin ajiye jarabawa bayan ta yi nasarar lashe jarabawar.
Duk da cewa Malamin Dakta Anthony Agbegbedia ya tafka babban laifi amma jami'ar na kaucewa batun domin gudun bata sunanta a idon duniya.
Tun dalibar ta na aji 3 ne malamin ke bibiyarta da iskanci har ta shiga ajin karshe amma bai yi nasara ba.
Mahaifin dalibar dai ya mika korafinsa a rubuce ga hukumomin jami'ar tun ranar 20 ga watan Agusta, inda ya zargi malamin da kokarin lalata masa diyarsa.