
Sakamakon tsadar rayuwa musamman tsadar litar man fetur a Najeriya bayan cire tallafin mai da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta yi, 'yan kasar na ci gaba da fama da matsin tattalin arziki ta ko ina.
Bisa al'ada, 'yan Najeriya daga yankin arewacin kasar kan tafi yankin kudanci domin neman na kansu a jihohin kidu maso yammacin da kudu maso gabaci da kudu maso kudancin kasar.
'Yan arewaci musamman 'yan arewa maso yammacin kasar daga jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Katsina da Jigawa na zuwa jihar Legas shekara aru-aru domin ayyukan leburanci.
Sakamakon tsadar kudin mota wanda tsadar man fetur ce ta haddasa, da yawan 'yan arewacin kasar ba sa iya biyan kudin mota zuwa kudancin Najeriya kamar yadda su ka saba a shekarun baya.
Wannan hoto ne da ke nuna 'yan jihar Sakkwato masu zuwa birnin Lagos a daure da igiya a jikin wata mota, inda su ke biyan kudaden da babu yawa domin su tafi Lagas.
Da dama daga cikin 'yan jihohin da ke zuwa birnin Legas ba za su iya biyan kudaden kujerun mota zuwa birnin Ekon ba a yanzu sakamakon tsadar kudin mota, duba da nisan tafiyar musamman daga jihar Sakkwato zuwa Legas.
A baya dai kayayyakin buhuna da dabbobi da makamancin wadannan ake sawa a bayan motoci sa'annan a daure da igiya, amma yanzu mutane ake daurewa da igiya kamar awaki domin kai su kudancin kasar sakamakon talauci.