
Gwamnan jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya Seyi Makinde, ya maimaita cewar zabukan shekara ta 2027 zai kasance mai zafi a tarihin Najeriya.
Gwamna Makinde ya ce, zaben tsakanin yan Najeriya ne da jam'iyyar APC mai mulki, ba tsakanin APC da jam'yyar adawa ta PDP ba ne.
Seyi Makinde ya ce, yan Najeriya ne kadai za su zabi abinda zai zama musu mai amfani ko akasin haka.
Makinde ya ce, wahalhalu da yan kasar ke ciki shi zai karkata akalarsu zuwa abinda ya kamata da wandanda suka kamata su zaba a zaben mai zuwa.
Gwamna Seyi Makinde ya kara da cewa lokaci ya wuce da yan Najeriya za su cigaba da wahala, inda ya ce akwai bukatar su samarwa kansu mafita.
A daya bangaren, gwamna Makinde ya ja hankalin 'ya'yan babbar jam'iyyarsa ta adawa ta PDP da su zama tsintsiya madaurinki daya domin kawo karshen rarrabuwar kai tsakanin yan jam'iyyar.
Yin hakan a cewar gwamna Makinde zai karawa jam'iyyar karfi da azama wajen tunkarar abubuwan da ke gabanta.