• 17 Jun, 2025

Ya Zama Dole Najeriya Ta Yi Taka Tsan-Tsan Da Bankin Lamuni—Cewar Farfesa Jaga

Ya Zama Dole Najeriya Ta Yi Taka Tsan-Tsan Da Bankin Lamuni—Cewar Farfesa Jaga

1000000838.jpg

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya Farfesa Attahiru Jega ya gargadi gwamnatin tarayya dangane da karban shawarwarin bankin lamuni da banki duniya.

Farfesa Jaga ya ce ba laifi ba ne idan gwamnatin ta yi alaka da su amma ta yi taka tsan-tsan yayin hulda da su domin gujewa tsunduma ciki matsalar din-din-din.

Jega ya furta haka ne yayinda ya ke jawabi a wajen taron shekara-skekara kan tattalin arziki da shugabanci nagari.

Jega ya ce cin bashi da karban shawarwari daga hukumomin bazai kawo karshen matsalolin kasar ba.

Babbar matsalar Najeriya a cewar Farfesa Jega ita ce rashin shugabanci, inda ya ce, shugabanni ba su shirya yin jagoranci na gari ba.

Jega ya kara da cewa daukan shawarwari daga hukumar lamuni da ma bankin duniya su suka janyo Shugaba  Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur da ma karya darajar kudin Najeriya, inda yan kasar ke cikin mummunar yanayi.

Duk da cewar Shugaban bankin lamunin a yankin Africa Abebe Selassie ya karyata hannun bankin lamunin cikin cire tallafin mai a Najeriya, Jega ya ce gwamnatin Najeriya ta kiyayi hukumomin biyu.

 

Ahmed Abubakar

How puzzling all these changes are! I'm never sure what I'm going to turn into a tidy little room.