
Tsohon mataimakin sakataren Amurka kan harkokin Afrika Tibor Nagy ya ce gwamnatin Najeriya ta yi hankali da da sabuwan kungiyar 'yan ta'adda da ta bullo a jihar Sakkwato.
Nagy ya ce Kungiyar mai suna Lakurawa babbar barazana ce a Najeriya duba da rashin tsaro sa kasar ke fama da shi sakamakon 'yan bindiga da 'yan kungiyar Boko Haram da ke addabar Najeriya.
Nagy ya ce kungiyar tuni ta fara tada hankalin jama'a ta hanyar gindaya wa mutane tsauraran dokoki wadanda hakan bazai yiwa kasar kyau ba.
Tibor wanda ya nuna damuwarsa ta shafinsa ta X a jiya Talata ya ce, akwai bukatar Najeriya ta yi taka-tsan-tsan, duba da yadda kungiyar Boko Haram ta fara, inda a karshe ta zama babbar matsala a kasar.
Nagy ya ce dole gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye domin dasa aya wa kungiyar ta Lakurawa kafin lokaci ya kure, kamar yadda kungiyar Boko Hsram ta lalata arewacin kasar.
Mista Tibo Nagy ya ce bullar Kungiyar Lakurawa na nuna karuwar matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da su, don haka ya zama dole gwamnatin kasar ta tashi tsaye domin kawo karshe kungiyar Lakurawa a arewacin kasar.